22 Mayu 2025 - 11:15
Source: ABNA24
Shaikh Zakzaky H Ya Gana Da Ɗaliban Fudiyyah + Hotuna

Jiya laraba 23 ga watan DhulQa'ada, 1446H (21/05/2025) Jagora Shaikh Ibraheem Zakzaky (H), kamar yadda aka saba kowacce shekara ya gana da wasu daga cikin ɗaliban makarantun Fudiyya daban-daban waɗanda suke shirin yin bikin haddar Alkur’ani Mai girma, a gidansa da ke Abuja.

Kamfanin dillancin labaran ƙasa da ƙasa na Ahl-Bait As -Abna- ya habarta cewa: A yayin ziyarar Jagora (H) ya fara taya su jajen shahadar Imami na 8 cikin jerin Imaman shiriya daga tsatson Manzon Tsira (S), wanda ya yi shahada a ranar irin ta yau. Jagora ya bada takaitaccen tarihin Imam Ridha da yadda mai mulki a zamanin (wato Mamun) ya yi sanadiyar shahadar sa.

Jagora (H) ya ƙarfafi ɗaliban tare da yi musu nasihar su dage iyakar kokarinsu wajen ganin sun yi aiki da abinda su ka karanta na daga Alkur'ani mai girma.

Daga Ofishin Jagora Sheikh Ibrahim Alzakzaky H

23/DhulQaada/1446

21/05/2025

Your Comment

You are replying to: .
captcha